Bangaren kasa da kasa; a karon farkom a bude wani gurin sayar da kayan sanyawa irin na Musulunci ga mata masu son suturta kansu a garin Sidni na kasar Ostriya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci na Iran ikna bayan ta jiyo daga majiyar watsa labarai ta Muhit ta watsa rahoton cewa; a karon farkom a bude wani gurin sayar da kayan sanyawa irin na Musulunci ga mata masu son suturta kansu a garin Sidni na kasar Ostriya.Wannan wani babban ci gaba ne aka samu ta fuskar kayayyakin sanyawa irin na Musulunci a kasashen turai musamman idan aka yi la'akari da yadda ake fuskantar matsala dangane da sanya hijabi a tsakanin gwamnatocin nahiyar Turai.
581582