Bangaren kasa da kasa; da dama daga cikin abubuwa masu muhimmanci da daraja na addini da akhalaki da fahimta ta hakika ta addinin Musulunci a Afrika sun kawar amma jami'ar Almustapha (SWA) Al'alamiya ta yi taka kokarin wajen yada addinin Musulunci a Afrika da taka muhimmiyar rawa ta bangaren addini.
Hamid Amuri wakilin jami'ar Almustapha (SWA) Al'alami a Guine Konakry a wata tattaunawa da ta hada shi da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna dangane da wannan labari ya bayyana cewa; da dama daga cikin abubuwa masu muhimmanci da daraja na addini da akhalaki da fahimta ta hakika ta addinin Musulunci a Afrika sun kawar amma jami'ar Almustapha (SWA) Al'alamiya ta yi taka kokarin wajen yada addinin Musulunci a Afrika da taka muhimmiyar rawa ta bangaren addini.Shi dai Hamid Amuri ya zauna a Niger na tsawon shekaru biyu, a Malawi Shekaru uku da watanni biyar,watanni uku a Burkina da kuma a halin yanzu yake a ksar Guine Konakry a matsayin wakilin jami'ar Almustapha (SWA) al'alami a wannan kasa.
581520