Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta konyamuftlugu ta watsa rahoton cewa;
; ma'aikatar da ke kula da harkokin addini a kasar Turkiya ce za ta shirya taron sani da faimtar Kur'ani a ranar juma'a ashirin da daya ga watan Khurdad na wannan shekara ta hijira shamsiya ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a garin Konya. Wannan taro dai a shirya shi ne da zumma girmama wannan shekara ta dubu biyu da goma miladiya da aka bata sunan shekarar Kur'ani Mai Girma a wannan kasa bayan shekaru dubu daya da dari hudu suka gabata da sabko da Kur'ani a birnin Makka da Madina.
584761