Bangaren kasa da kasa: hukumar Asesko a wani kokari na raya al'adun matasa Palasdinwa sun goyi bayan shirin fasaha a birnin Kudus.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta kusa da hukumar kula da al'adu ta kasashen musulmi Isesko ta watsa rahoton cewa; : hukumar Asesko a wani kokari na raya al'adun matasa Palasdinwa sun goyi bayan shirin fasaha a birnin Kudus. Wannan mataki da hukumar ta Esesko ta dauka ya yi daidai musamman a daidai wannan lokaci da aka fi bukatar tallafawa matasan Palsdinu fiye da wani lokaci day a gabata idan aka yi la'akari makircin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan matasan Palasdinu.
587040