Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga Saphirnews ta watsa rahoton cewa; a birnin Paris ne a ranar takwas ga watan Khurdad na wannan shekara aka gudanar da taron karawa juna ilimi kan salon yin tafsirin kur'ani mai girma a masallacin Usamn da ke birnin na Paris. Wadanda suka halarci gurin wannan taro sun yi masanyar tunani da nazari kan wannan bangare da yadda kowa yake kollon lamari da yadda za a magance matsalolin da ke addabar wannan bangare.
587958