Cibiyar da ke kula da hankokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ce ta bayyana cewa;Pira minister Rajab Tayyib Urgugan ya yanke ziyarar da ya ke yi a yankin Latin Amerika domin komawa gida saboda ya bi diddigin abinda ya ke faruwa.
Rahotanni suna nuni da cewa mutane goma sha biyar daga cikin wadanda su ka yi shahada 'yan kasar Turkiya ne.
Pira ministan kasar Turkiya ya yi kira ga kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato da ta yi taron gaggawa domin tattauna hatsarin da ke tattare da wannan harin.
Bugu da kari Kasar ta Turkiya ta kirayi jakadanta da yake a Tel Aviv domin ya koma gida.
589291