Kamfanin dillancin labaran Sharqul-Awsad na kasar Masar ne ya watsa labarin cewa; A jiya talata shugaban kasar Masar Husni Mubarak ya bada umurnin bude mashigar Rafah saboda dalili na jin kai. Wannan umurni na shugaban kasar Masar ya zo ne a matsayin matakin kwantar da hankalin al'ummar kasar Masar da suka fusata sakamakon harin ta'addancin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan jiragen ruwan da suke dauke da kayayyakin agaji zuwa yankin Zirin Gaza kuma al'ummar kasar ta Masar suna daukan gwamnatin kasarsu a matsayin daya daga cikin wadda take da hannu a killace yankin na Zirin Gaza.
Mahukuntan na kasar Masar sun bayyana cewa an bude mashigar ta Rafah ce domin shigar da kayayyakin agaji da suka hada da abinci da magunguna ga Palasdinawa da suke cikin halin kaka-ni-ka yi a yankin Zirin Gaza sakamakon killace yankinsu da aka yi tsawon shekaru.
589705