IQNA

Maida Martani Kasashen Duniya Kan Harin HKI

15:11 - June 02, 2010
Lambar Labari: 1933639
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta fara sakin masu rajin kare hakkin bil-Adama da 'yan jaridu da ta kame bayan harin ta'addancin da sojojinta suka kai kan jiragen ruwan da suke dauke da kayayyakin agaji zuwa yankin Zirin Gaza da nufin kawo karshen killace yankin da aka yi tsawon shekaru.
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta saki masu rajin kare hakkin bil-Adama 46 da suka fito daga kasashen Turai ta hanyar sanya su a jiragen sama domin mai da su kasashensu, yayin da ta saki wasu da yawansu ya kai 121 ta hanyar mika su ga kasar Jordan, kuma tuni gwamnatin H.K.I ta mikawa kasar Masar 'yan kasarta guda goma daga cikin mutanen da ta kame, sannan gwamnatin ta H.K.I ta bayyana cewa zata ci gaba da tsare wasu daga cikin mutanen da ta kame domin gurfanar da su a gaban kotu kan zargin cutar da sojojin H.K.I a lokacin da sojojin suka kai farmaki cikin jiragen ruwan da suke dauke da kayayyakin agaji zuwa yankin Zirin Gaza.

A ranar litinin da ta gabata ce sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai harin ta'addanci kan jiragen ruwan da suke dauke da kayayyakin agaji zuwa yankin Zirin Gaza da aka killace inda suka kashe masu rajin kare hakkin bil-Adama akalla 19 tare da jikkata wasu da dama sannan suka kame dukkanin mutanen da suke cikin jiragen da suka fito daga kasashe 42 na duniya.



589574
captcha