A jiya talata ce shugaban kasar Nicaragua Daniel Ortega ya gabatar da jawabi ta hanyar tashar talabijin din kasar inda a ciki ya bayyana cewa daga jiya talata kasarsa ta dakatar da duk wata alakar jakadanci da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila. Daniel Ortega ya kara da cewa kaddamar da hari kan jiragen ruwan da suke dauke da kayayyakin agaji karya dokokin kasa da kasa ne kuma karya hakkin bil-Adama ne.
Daniel Ortega ya kuma bayyana cewa kasarsa tana jaddada goyon bayanta ga al'ummar Palasdinu kuma tana kira ga kawo karshen killace yankin Zirin Gaza da aka yi. Idan za a iya tunawa a watan disamban shekara ta 2009 kasashen Venezuela da Bolivia sun dauki matakin yanke alakar jakadanci da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sakamakon hare haren wuce gona da iri da sojojin H.K.ta Isra'ila suka kai yankin Zirin Gaza. Ita kuwa kasar Cuba tun a shekara ta 1973 ta yanke alakar jakadancinta da gwamnatin ta haramtacciyar kasar Isra'ila.
589557