Kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarta cewa ministan harkokin wajen kasar ta Norway Jonas Gahr ya kira yi kungiyar tarayyar Turai da ta ci gaba da gudanar da alaka da kasar Sudan domin hakan yana da muhimmanci kafin gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a dangane da makomar yankin kudancin kasar.
Jonas Gahr ya kuma bayyana jin dadinsa kan goyon bayan da kungiyar tarayyar Turai ke nunawa ga shirin kada kuri'ar jin ra'ayin jama'ar kudancin kasar Sudan kan amincewa da ci gaba da kasancewa cikin Sudan ko kuma ballewa, sannan ya bukaci kungiyar ta tarayyar Turai da kada ta yi sakaci har batun neman kame shugaban kasar Sudan ya zame kafar ungulu ga shirin neman warware rikicin dake tsakanin gwamnatin Sudan da yankin kudancin kasar.
589933