IQNA

Turkiya Na Ci Gaba Da Maida Martani

15:10 - June 02, 2010
Lambar Labari: 1933643
Pira ministan kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdogan ya bayyana harin da sojojin yahudawan Sahayoniya su ka kaiwa jragen ruwan agaji da cewa ayyukan ta'addanci ne na gwamnati.

Pira minister Rajab Tayyib Urgugan ya yanke ziyarar da ya ke yi a yankin Latin Amerika domin komawa gida saboda ya bi diddigin abinda ya ke faruwa.
Rahotanni suna nuni da cewa mutane goma sha biyar daga cikin wadanda su ka yi shahada 'yan kasar Turkiya ne.
Pira ministan kasar Turkiya ya yi kira ga kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato da ta yi taron gaggawa domin tattauna hatsarin da ke tattare da wannan harin.
Bugu da kari Kasar ta Turkiya ta kirayi jakadanta da yake a Tel Aviv domin ya koma gida.




589982



captcha