IQNA

Bincike A Faransa Kan Musulunci Da Yanayi

Bangaren kasa da kasa; a ranar ashirin da tara ga watan Khurdad n awannan shekara ta dubu daya da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin Liyon na kasar Faransa za a gudanar da taro day a shafi bincike kan Musulunci da kuma yanayi da muhalli.



Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga journee-culturelle ta watsa rahoton cewa; a ranar ashirin da tara ga watan Khurdad n awannan shekara ta dubu daya da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin Liyon na kasar Faransa za a gudanar da taro day a shafi bincike kan Musulunci da kuma yanayi da muhalli.
Wannan taro yana da matukar muhimmanci musamman idan aka yi la'akari da halin da duniya ke ciki a yau da kuma wannan lokaci na tabarbarewar muhalli da yanayi da duniya ke ciki da kuma irin matsalolin da dumamar yanayi ke haddasawa da bala'o'in da hakan ke jawo wa.

591640