IQNA

Baje Kolin Kayan Kira Na Kasashen Musulmi A Masar

17:17 - June 07, 2010
Lambar Labari: 1935742
Bangaren kasa da kasa;a karo na uku za a gudanar da taron kamfanoni da masana'antu na kasashen musulmi da ke mambobi a cikin kungiyar hadin kan kasashen musulmi da za a fara gudanarwa daga ranar sha tara zuwa ashirin da biyu ga watan Khurdad din nan da muke ciki na hijira shamsiya.



Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta events.alriyadh.org.sa ta watsa rahoton cewa; a karo na uku za a gudanar da taron kamfanoni da masana'antu na kasashen musulmi da ke mambobi a cikin kungiyar hadin kan kasashen musulmi da za a fara gudanarwa daga ranar sha tara zuwa ashirin da biyu ga watan Khurdad din nan da muke ciki na hijira shamsiya. Wannan kasuwar baje koli cibiyar kasuwanci da ci gaban kasashen musulmi ICDT da kuma hadin guiwar hukumar shirya kasuwannni baje koli ta kasar Masar EECA suka shirya karkakshin kulawar ma'aikatar yawan shakatawa ta Masar.


592338
captcha