Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Manilla Bulletin ta watsa rahoton cewa; taro kan Musulunci addini ne na sulhu da aka fara a ranar asabar sha biyar ga watan Khurdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a garin Manil babban birnin kasar Pilifines.Wannan taro kungiyar da ke kula da harkokin addini a wannan kasa ce ta shirya da zummar fadakar da hankulan jama'a kan muhimmancin zaman lafiyar da kuma yadda addinin Musulunci ke sahun gaba a tsakanin sauran addinai a duniya wajen hadin kai da zaman lafiya.
592274