IQNA

Gasar Karatun Kur'ani Ta Kasa Da Kasa Karo Na Sha Takwas A Masar

17:12 - June 07, 2010
Lambar Labari: 1935746
Bangaren kasa da kasa; taron kasa da kasa karo na sha takwas na karatun kur'ani a kasar Masar ga matasa yan kasa da shekaru ashirin da biyar da za a fara daga sha bakwai zuwa ashirin da biyar ga watan Ramadan a birnin Alkahira fadar mulkin Masar.



Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta ICCUK ta watsa rahoton cewa; taron kasa da kasa karo na sha takwas na karatun kur'ani a kasar Masar ga matasa yan kasa da shekaru ashirin da biyar da za a fara daga sha bakwai zuwa ashirin da biyar ga watan Ramadan a birnin Alkahira fadar mulkin Masar. Wannan gasar karatun kur'ani mai girma ma'aikatar da ke kula da harkokin addini a wannan kasa ta masar ta shirya domin karfafawa matasa karfin guiwa wajen harda da karatun kur'ani mai girma.

592192
captcha