IQNA

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi Ta Bukaci Yanke Alaka Da HKI

16:58 - June 08, 2010
Lambar Labari: 1936412
Bangaren kasa da kasa :ministocin harkokin kasashen da ke cikin kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar lahadi sha shidda ga watan Khurdad ta shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara sun fitar da wani bayani na bukatar kasashen musulmi da su yanke hulda da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.


Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar le Figaro ta watsa rahoton cewa; ministocin harkokin kasashen da ke cikin kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar lahadi sha shidda ga watan Khurdad ta shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara sun fitar da wani bayani na bukatar kasashen musulmi da su yanke hulda da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.Wannan taron ministocin harkokin wajen kasashen musulmin ya biyo bayan taron da suka gudanar a birnin Jidda na kasar Saudiya da kuma suka yi Allah wadai da harin ta'addancin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai wa ayarin masu rajin kare hakkin dan adam a kokarinsu na intar da yankin zirin Gaza daga killacewa haramtacciyar kasar Isra'ila.



593072
captcha