Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga kamfanin dillancin labarai na muzin ta watsa rahoton cewa; a karo na takwas aka kaddamar shirin addini da al'adu a lokacin hutu na musamman ga mata a cibiyar koyar da kur'ani mai girma a garin Sihat a lardin Kutaif na kasar saudiya. Ana faraa ne da koyar da kananan yara mata yan shekaru shidda zuwa bakwai yin salla da hukumce-hukumce na addini kafin su kai ga shekarun takalifi.
592733