Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyara watsa labarai ta Muhit ta watsa rahoton cewa; : hadin guiwar malaman addini a Sudan sun fitar da bayanin da ke cewa karyawa da kawo karshen killacewar da aka yi wa yankin zirin gaza da sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi wajibe na shari'a a kawo karshensa. A cikin sanarwa da suka fitar sun bukaci kasashen musulmi da na larabawa da su kawo karshen duk wata dangantaka da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila bayan harin da ta kai wa ayarin masu kare hakkin dan adam da ke kokarin kawo karshen killacewar da suka yi wa yankin Zirin gaza.
592813