Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga yeniasya ta watsa rahoton cewa; an kawo karshen gasar harda da karatun kur'ani mai girma karo na sha biyu a jiya asabar sha takwas ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a masallacin Ayub Sultan a garin Langenfeld na kasar Jamus. Wannan gasar da ofishin da ke kula da harkokin addini a ofishin jakadancin kasar Turkiya a Barlin ya shirya tare da halartar kungiyoyi da daman a yan turkiya da musulmi da ke zaune a kasar ta jamus.
594151