IQNA

Shirin Tarjamar Hadisai Na Annabi (SWA) Da Yarurruka A Saudiya

Bangaren kasa da kasa; Abdul Aziz Khuja ministan al'adu da watsa labarai na Saudiya shi ne ya bada labarin fara wannan shiri na tarjama Hadisan Annabin Rahama (SWA) a cikin harsuna daban daban na duniya a Saudiya.


Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci tai ran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar Saudiya Ukkaz ta watsa rahoton cewa; Abdul Aziz Khuja ministan al'adu da watsa labarai na Saudiya shi ne ya bada labarin fara wannan shiri na tarjama Hadisan Annabin Rahama (SWA) a cikin harsuna daban daban na duniya a Saudiya. A ranar talata ne sha takwas ga watan Khurdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a lokacin bude bangare watsa shirye shirye na radiyo da talbijin na Jidda a cikin Internet AbdulAziz Khuja ya bada labarin cewa; ma'akatar al'adu ta saudiya na da niyar zabar komitin da zai gudanar da wannan aiki.


594167