Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga timeturk ta watsa rahoton cewa; a karo na biyu an gudanar da taron tarjamomin Kur'ani da shugabannin mujallar zindigi Kur'amni tare da kungiyar Ukba kuma a ranar talatar da ta gabata ce aka kawo karshen wannan taro a birnin Istambul na kasar Turkiya. Wannan taro an kasa shi gida uku kashi na farko ya shafi irin matsalolin da masu tarjamar Kur'ani kr fuskanta a cikin harshen Turkanci na biyu matsaloli da masu tafsiri ke fuskanta a cikin harshen Turkanci sai kuma kashi na uku Kur'ani da hanayr sanin ma'anonin ayoyinsa.
594229