IQNA

Taron Kasa Da Kasa Na Masana Ilimin Tauraro A Tsarin Musulunci

Bangaren kasa da kasa; an gudanar da taron kasa da kasa na masana ilimin tauraro da rawar da suke takawa a tarihin duniya kuma wannan taro nasu an gudanar da shi ne a ranekun sha bakwai da sha takwas ga watan Khurdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin Istambul fadar mulkin kasar Turkiya.


Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta IRCICA ta watsa rahoton cewa; an gudanar da taron kasa da kasa na masana ilimin tauraro da rawar da suke takawa a tarihin duniya kuma wannan taro nasu an gudanar da shi ne a ranekun sha bakwai da sha takwas ga watan Khurdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin Istambul fadar mulkin kasar Turkiya.Wannan taro cibiyar masu bincike kan tarihi da cibiyar da ke kula fasaha da al'adu na kungiyar hadin kan kasashen musulmi IRCICA da kuma bangaren kula da al'adu a ma'aikatar magajin gari nan Istambul suka shirya.



594240