IQNA

Wata Kotun Qatar Ta Daure Wata Mata Da Ta Wulakanta Kur'ani

14:00 - June 12, 2010
Lambar Labari: 1938163
Bangaren kasa da kasa; Wata kotu a kasar Qatar ta yanke hukuncin shekaru bakwai a kanta wata mata 'yar kasar Ireland bayan da ta wulakanta kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga wani shafin internet na kasar Qatar an bayyana cewa, wata kotu a kasar qatar ta yanke hukuncin shekaru bakwai a kanta wata mata 'yar kasar Ireland bayan da ta wulakanta kur'ani mai tsarki. Bayanin ya ci gaba da cewa tun kimanin watanni tara da suka gabata wannan mata ta yi wurgi da littafin alkur'ani mai tsarki a cikin filin dafka da tashin jiragen sama na birnin Doha, lamarin da ya sanya aka kameta tare da tsare ta.595198

captcha