Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga wata jaridar Saudiyya an habarta cewa, idan Allah ya kai mu gobe za a fara gusdanar da wani zaman taro da baje kolin kayayyakin tarihin musulunci a birnin Sana na kasar Yeman. Daga cikin muhimman abubuwa da wannan taro zai mayar da hankali kansu akwai tattaunawa tsakanin bangarorin da sue halartar taron daga kasashen duniya musamman ma na musulmi, ta yadda hakan zai bayar da damar kara fahimtar juna tsakaninsu.595180