IQNA

Tahrirul Wasila An TarjamaSa A Cikin Harshen Turkanci Na Istambul

Bangaren al'adu da fasaha: a karo na biyu an tarjama littafin Tahrirul Wasila karo na biyu a cikin harshen turkancin Istambul kuma karamin ofishin jakadancin Iran ne a Istambul ya doki nauyin bugawa domin tuni da asr din Imam Khomeini ®.



Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna daga reshenta da ke hukumar da ke kula da harkokin al'adu ya watsa rahoton cewa; a karo na biyu an tarjama littafin Tahrirul Wasila karo na biyu a cikin harshen turkancin Istambul kuma karamin ofishin jakadancin Iran ne a Istambul ya doki nauyin bugawa domin tuni da asr din Imam Khomeini ®.Abdallah Un Alan ne ya tarjama a cikin harshen Turkanci na Istambul kuma gidan buga littafai na Ihsan ne ya buga guda dubu daya da dari biyar da kuma kowane littafi daya ya kumshi shafi dari hudu da tamanin.


595473