Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani day a nakalto daga shafin internet na iaba-austin an habarta cewa, Ana shirin gudanar da wani babban taron maulidi na iMam Muhammad Baqir (AS) a garin Autin na cikin jahar Texas na kasar Amurka, wanda wata cibiyar musulmi ta shirya.
Bayanin ya ci gaba da cewa, cibiyar da ta shirya gudanar da taron cibiya ce da ke kula harkokin musulunci da kuma tafarki ahlul bait musamman a cikin kasar. Daruruwan musulmi ne za su samu halartar taron. 595651