Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wani labari da tashar yada labarai ta rasid ta bayar ya yi nuni da cewa, daya daga cikin malaman mabiya mazhabar shi'a na kasar Saudiyya Taufiq Saif ya bayyana cewa, babban abin da suke bukata shi ne a daina nuna musu banbanci a kasar. Ya ci gaba da cewa suna son gwamnatin kasar ta rika ba su dukkanin hakkokinsu na 'yan kasa maimakon irin yadda ake yi musu a halin yanzu, inda ya bayyana cewa ba a yi musu adalci a cikin dukkanin lamurra a matsayin na 'yan kasa masu cikakken hakki. 595633