Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Wata cibiyar yada ilimi da raya al'adun musulunci a yankin Katif na kasar Saudiyya na shirin fara gudanar wani shirin horar da mata kan ilmin addinin musulunci.Bayanin wanda tashar watsa labarai ta rasid ce ta bayar da shi, ya yi nuni da cewa dukkanin masu gudanar da shirin sun kammala shirye-shiryensu, kuma za a mayar da hankali ne kan ilmomin fikihu da usul da akida. Cibiyar ilimi ta khadijatul kubra ce ta dauki nauyin gudanar da shirin. 595516