IQNA

Hussain Baharvand Ne Ya Samu Kyautar ISESCO A Bana

20:19 - June 13, 2010
Lambar Labari: 1939077
Bangaren kasa da kasa; Hussain Baharvand wanda daya ne daga cikin mambobin kwamitin bincike na kungiyar yada al'adu da ilmin musulunci shi ne ya samu kyautar wannan kungiya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na kungiyar yada al'adu da ilmin musulunci ta kasa da kasa cewa, Hussain Baharvand wanda daya ne daga cikin mambobin kwamitin bincike na kungiyar yada al'adu da ilmin musulunci shi ne ya samu kyautar wannan kungiya ta wannan shekara. Bayanin ya ci gaba da cewa ya samu wannan kyautar ne sakamakon kokarin da yake yi wajen fadada bincike a dukkanin bangarori, musamman na addini da za su amfanar da musulmi. 595481

captcha