IQNA

Tashar Radio Ta Aljazeera Za Ta Watsa Gasar Kur'ani Kai Tsaye

20:19 - June 13, 2010
Lambar Labari: 1939078
Bangaren kasa da kasa; Tashar radio ta aljazeera za ta watsa gasar karatun kur'ani mai tsarki kai tsaye, wadda za a gudanar a cikin watan Ramadan mai zuwa a birnin Doha na kasar Qatar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar radio ta aljazeera za ta watsa gasar karatun kur'ani mai tsarki kai tsaye, wadda za a gudanar a cikin watan Ramadan mai zuwa a birnin Doha na kasar Qatar. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasar karatun kur'ani ta kebanci kanan ya ne kawai da shekarunsu ba su wuce takwas zuwa goma sha uku ba, kuma dukkaninsu za su fito daga kasashen larabawa na yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka. 595449


captcha