Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na arabonline an habarta cewa, wata tawaga daga kasar Rasha ta bukaci gudanar da wani baje koli na kur'ani mai tsarki a kasar Saudiyya, bayan da ta bayar da kyautar wani kur'ani ga sarkin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa tawagar na neman hakan da nufin kara karfafa dangantaka tsakanin al'ummomin kasashen biyu. 595443