IQNA

Malaman Makka Sun Yi Allawadai Da Gubatattun Fatawoyi

14:01 - June 14, 2010
Lambar Labari: 1939531
Bangaren kasa da kasa; Wasu daga cikin malaman addinin muslunci na birnin Makka sun yi kakkausar suka kan fitar da fatawoyi marassa kan gado da wasu daga cikin malaman wahabiyawa ke yi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na Nasij an habarta cewa, wasu daga cikin malaman addinin muslunci na birnin Makka sun yi kakkausar suka kan fitar da fatawoyi marassa kan gado da wasu daga cikin malaman wahabiyawa ke yi. Malaman birnin Makka sun kafa dalili ne da fatawowi da wasu daga cikin wadanda suke kiran kansu malamai a kasar suke bayarwa, wanda bisa akidarsu hakan ya saba wa abin da suka sani. 596233



captcha