IQNA

Samun Fahimtar Juna Tsakanin Sunna Da Shi'a Ba Ajiye Akida Ba ne

14:01 - June 14, 2010
Lambar Labari: 1939536
Bangaren kasa da kasa; Shugaban ofishin da ke kula lamurran Iran a kasar Masar Ali Juma'a ya yi kira ga dukkanin bangarorin musulmi sunna da shi'a da su hada kai domin fuskantar abin da ke gabansu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran muhit ya habarta cewa Shugaban ofishin da ke kula lamurran Iran a kasar Masar Ali Juma'a ya yi kira ga dukkanin bangarorin musulmi sunna da shi'a da su hada kai domin fuskantar abin da ke gabansu. Bayanin ya ci gaba da cewa malamin ya mayar da hankali wajen tabbatar wa musulmi cewa banbancin fahimta ba zai taba hana a hadu domin yi wa Musulunci aiki ba, kuma haduwar sunna da shi'a bay a nufin wani bangare daga cikinsu ya ajiye fahimtarsa ko akidarsa. 596285
captcha