Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Jakarta post ta habarta cewa a jiya ne aka kammala gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Indonesia, taron da ya samu halartar manyan jami'an gwamnatin da suka hada da mataimakin shugaban kasa. Rahoton ya ci gaba da cewa mataimakin shugaban kasar ya yaba da yadda makaranta kur'ani mai tsarki a kasar suke mayar da hankali wajen bunkasa harkokin karatun kur'ani da kuma hardarsa. 596350