IQNA

Rashin Kulawar Larabawa Da Musulmi Na Kara Rauninsu

19:34 - June 14, 2010
Lambar Labari: 1939801
Bangaren kasa da kasa; Musulmi da larabawa na nuna rashin kulawa a cikin lamurran da suka shafe su a matsayin siyasar duniya, wanda hakan ne babban dalilin da yasa suka yi rauni.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban sakataren cibiyar quds ta sarkin kasar Jordan Abdullah Kan'an ya bayyana cewa; musulmi da larabawa na nuna rashin kulawa a cikin lamurran da suka shafe su a matsayin siyasar duniya, wanda hakan ne babban dalilin da yasa suka yi rauni. Bayanin ya ci gaba da cewa babba abin bakin ciki ne yadda da dama daga cikin musulmi suka gafala dangane da halin da masallacin qods yake ciki a halin yanzu, musamman ma a cikin lokacin da yahudawan sahyuniya suke ta kara matsa kai mi wajen bakanta surar Musulunci. 596504



captcha