Bangaren kasa da kasa: a kasar Turkiya a birnin Istambul ne za a gudanar da gasar waka da iya rubutu da aka yi wa taken maulidun Ka'aba da cibiyar al'adu da bada horo a masallacin Zainabiya ta shirya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta masallacin Zainabiya a birin Istambul ta watsa rahoton cewa; a kasar Turkiya a birnin Istambul ne za a gudanar da gasar waka da iya rubutu da aka yi wa taken maulidun Ka'aba da cibiyar al'adu da bada horo a masallacin Zainabiya ta shirya. Wannan gasar ta z one a daidai lokacin zagayowar irin wannan rana ta haifuwar Hadarat Imam Ali (AS) kuma masu bukatar halartar wannan gasa har zuwa uku ga watan Tir na iya rubuta sunayensu.
597011