IQNA

An Gudanar Da Gasar Kiran Sallah A Tsibirin Burnai

15:57 - June 15, 2010
Lambar Labari: 1940408
Bangaren kasa da kasa; A jiya ne aka gudanar da gasar kiran sallah a tsibirin Burnai wadda ta kebanci matasa babban masallacin babban Mantiri fadar mulkin tsibirin na Burnai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da yanakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bru-Drict an habarta cewa, a jiya ne aka gudanar da gasar kiran sallah a tsibirin Burnai wadda ta kebanci matasa babban masallacin babban Mantiri fadar mulkin tsibirin na Burnai. Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin wadanda suka shiga gasar matasa ne kuma an kuma kasa bangarorin gasar zuwa kashi-kashi ta yadda za su damar daukar bangaren da suka fi kwarewa a cikinsa. Daga karshe an zabi uku daga cikinsu a matsayin wadanda suka lashe gasar. 597354



captcha