Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na Bur-Direct ya habarta cewa, yanazu haka dai an shiga bangaren karshe na gasar karatun kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Begavan na Burnai, wadda ke samun halartar makaranta kur'ani mai tsarki na kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasar karatun kur'ani tana dagy daga cikin irinta da a aka taba gudanarwa a kasar, wadda aka fitar da makaranta takwas da suka kai ga mataki na karshe. 596996