IQNA

Taro Kan Tasirin Kur'ani Wajen Magance Matsalolin Hankali

15:55 - June 15, 2010
Lambar Labari: 1940418
Bangaren kasa da kasa; A yau ne za a gudanar da wani zaman taro da zai bahasi kan tasirin kur'ani mai tsarki wajen warware matsaloli da suka shafi hankali a garin Jazan na kasar Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na na yanar gizo na Muhit ya habarta cewa, a yau ne za a gudanar da wani zaman taro da zai bahasi kan tasirin kur'ani mai tsarki wajen warware matsaloli da suka shafi hankali a garin Jazan na kasar Saudiyya. Bayanin ya ci gaba da cewa ma'aikatar kula da al'adu da sadarwa ta kasar Saudiyya ita ce ta shirya gudanar da zaman taron wanda zai bahasi kan yadda kur'ani mai tsarki ke yin tasiri a lokacin da ake karanta a kan wasu matsaloli da suka shafi hanakali, wanda lokitoci sun tabbatar da hakan. 597180




captcha