IQNA

An Bayar Da Shawar Kafa Bangaren Al'adun Musulunci A Kuwait

15:55 - June 15, 2010
Lambar Labari: 1940419
Bangaren kasa da kasa; An gabatar da shawara ga majalisar dokokin kasar Kuwait dangane da samara da bangarorin kula da harkokin al'dun musulunci a dukkanin cibiyoyin ilimi na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Alrayi ta kasar Kuwait cewa, dan majalisar dokokin kasar kuma wakilin mabiya mazhabar shi'a na kasar a majalisa sayyid walid tabatabai ya gabatar da shawara ga majalisar dokokin kasar Kuwait dangane da samara da bangarorin kula da harkokin al'dun musulunci a dukkanin cibiyoyin ilimi na kasar. Ya ce ya gabatar da wannan shawara ne domin ganin irin tasirin da al'adu suke da shi a cikin zamantakewar jama'a, kuma kula da su zai taimaka matuka wajen yi matasa birki tare da dora su kan sahihin tafarki na musulunci, maimakon kwafar dabi'un turai.597143

captcha