Kamfanin dillancin iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar labarai ta Rasid cewa, an fara aiwatar da wani shiri horar da yara yan makarantun sakandare ilmomin ku'ani da sirar ma'aiki (SAW) a yankin Katif na mabiya mazhabar shi'a a kasar Saudiyya. Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin wannan shirin za a koyar da abubuwa da dama da suka hada koyon karatun kur'ani mai tsarki da nau'oin kira da kuma sirar manzo(SAW) gami da ilmomin akida da kuma ilmin sharia da sauran ilmomin musulunci, kuma za a gudanar da gasa kansu a karashen bazara. 597160