IQNA

Taron Kasa Da Kasa Na Jagororin Addini Na Duniya A Kanada

11:16 - June 16, 2010
Lambar Labari: 1940896
Bangaren kasa da kasa; taron kasa da kasa na jagororin addinai na duniya da za a gudanar a kasar Kanada daga ranar talatin da daya ga watan Khurdad zuwa biyu ga wannan Tir na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya.

Cibiyar da ke kula da harkokin da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga Winnipeg Free Press ta watsa rahoton cewa; taron kasa da kasa na jagororin addinai na duniya da za a gudanar a kasar Kanada daga ranar talatin da daya ga watan Khurdad zuwa biyu ga wannan Tir na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya. Kimanin shugabannin addinai tamanin da suka fito daga kasashen duniya za su halarci wannan taron jagororin addinai a duniya a kasar Kanada inda za su yi nazari da bincike kan lamurra da matsaloli da suka shafi hakkokin dan adam ,yancin addini da kuma rusha talauci daga tushe.


597645

captcha