IQNA

Za A Fara Karatun Khatmar Kur'ani A Masakllacin Manzo (SAW)

13:49 - June 16, 2010
Lambar Labari: 1941117
Bangaren kasa da kasa; Za a fara khatmar kur'ani mai tsarki a masallacin manzon Allah (SAW) da ke birnin Madina mai alfarma, wanda wasu daliban makarantun kur'ani na kasar Qatar za su gudanar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar kasar alraya cewa, za a fara khatmar kur'ani mai tsarki a masallacin manzon Allah (SAW) da ke birnin Madina mai alfarma, wanda wasu daliban makarantun kur'ani na kasar Qatar za su gudanar. Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka daliban na kasar Qatar sun birnin mai alfarma, wadanda shekarunsu bas u wuce 16 zuwa 20 ba, kuma za su kwashe kwanaki 40 cur suna gudanar da wannan khatma a masallacin mai tsarki.598106



captcha