Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na wocmes cewa, za a gudanar da wani zaman taro dangane da tawilin kur'ani mai tsarki da matanonin da aka rubuta na kur'ani, wanda jami'ar Barcelona ta kasar Spain ta shirya gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa za a gudanar da zaman taron ne a birnin Catalonia na kasar ta Spain, wanda masanin nan dan kasar Austaralia Ismail Albark ya yi kira da a gudanar, Masana da masu nazari daga jmi'oi daban-daban za su halarci wanann zaman taro. 598035