IQNA

Littafin Al'adun Musulunci Cikin Littafan Darasi A Rasha

13:49 - June 16, 2010
Lambar Labari: 1941122
Bangaren kasa da kasa; An saka littafin aladun musulunci a cikin littafan darasi a kasar Rasha, da zai hada da jami'oi da ma makarantun gaba da sakandare na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin yanar gizo na dunyabulteni an habarta cewa, za a saka littafin aladun musulunci a cikin littafan darasi a kasar Rasha, da zai hada da jami'oi da ma makarantun gaba da sakandare na kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa littafin wanda malaman addinin muslunci na kasar gami da malaman jamia suka rubuta, ya samu karbuwa a wajen hukummin ilimi na kasar ta Rasha, kuma tuni aka bayyana shi a cikin littafan da za a rika kyarwa a kasar domin bayar da dama ga dalbai su kara samun masaniya dangane da addinin musulunci. 598058


captcha