Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran irna na kasar Iran ya habarta cewa, a daidai lokacin da za a gudanar da bukuwan tunawa da ranar haihuwar Imam Ali (AS) ne za a bude karamin ofishin jakadancin Iran a birnin Najaf mai alfarma a Iraki. Bayanin ya ci gaba da cewa bude karamin ofishin jakadancin Iran a Najaf ya samu karbuwa daga manyan malaman addini na birnin gami da dalibai, kuma manufar bude shi ita ce sawwaka hanyoyin da masu ziyara a kasashen biyu suke bi domin ziyartar wurare masu tsarki. 598033