Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani zaman taro da ya hada ministocin harkokin tattalin arziki na kasashen musulmi a kasar Singapor, ministan harkokin kasuwanci da tattalin arziki na kasar Singapor Lim Hinkiam ya bayyana cewa tattalin arzikin kasashen musulmi na taimaka ma tattalin arzikin kasashen Asia. Bayanin ya ci gaba da cewa mnistan ya kara jadda wajabcin karfafa dangantaka ta bangarorin da dama musamman na tattalin arziki da kasuwanci tsakanin kasashen Asia da kuma kasashen musulmi. 597767