IQNA

Malaman Addini Sun Gudanar Da Zaman Taro Kan Gaza A Syria

19:16 - June 16, 2010
Lambar Labari: 1941306
Bangaren kasa da kasa; Kimanin malaman addinin Musulunci 500 gami da masu bincike da nazari a jami'oi da suka hada da musulmi da kiristoci ne suka gudanar da zaman taro kan Gaza a Syria.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Syria sana an bayyana cewa, kimanin malaman addinin Musulunci 500 gami da masu bincike da nazari a jami'oi da suka hada da musulmi da kiristoci ne suka gudanar da zaman taro kan Gaza a Syria. Bayanin ya ci gaba da cewa babban abin da taron ya mayar da hanakali kansa shi ne batun killace yankin zirin Gaza da haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi, tare da jadda wajabcin kawo karshen wannan killacewa. 598183



captcha