Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar kasar Qatar ta alraya cewa, shugaban cibiyar kula da harkokin kur'ani mai tsarki a kasar Qatar ya bayyana cewa za a gudanar da gasar iyalan mahardata kur'ani a birnin Doha na kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa a yayin gudanar da wannan gasa, wadda kanan yara da shekarunsu ba suwuce 7 zuwa 12 ba ne suke halarta, za a fitar da wadanda suka yi nasara a dukkanin bangarorin harda da kuma karatu.598140