Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daya daga cikin mambobin majalisar musulmin kasar Danmark sayyid Jafar Fatimi ya bayyana cewa, ana shirin kafa wata babbar cibiyar Musulunci a kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa sakamakon zane-zanen batuncin da aka yi ta yi a kasar na cin zarafin addinin Musulunci majalisar ta yanke shawarar kara fadada ayyukanta a kasar domin wayar da kan mutane dangane da addinin Musulunci da kuma koyarwarsa.598086